Bayanan sun nuna cewa jirage biyar sun tashi daga Filin Jirgin Sama na Birnin Panama, hudu kuma suna kan hanyarsu ta zuwa Filin Jirgin Sama na Caracas, yayin da na biyar ya ci gaba tafiya zuwa Suriname. Jirgin na shida ya shiga sararin samaniyar Venezuela daga Bogotá kafin ya sauka a Caracas.
Tsakanin 21 da 29 ga Nuwamba, an soke ko jinkirta jiragen sama 270 a Venezuela saboda gargadin Amurka. Filin Jirgin Sama na Duniya na Simón Bolívar ne ya fi tasirantuwa da hakan, inda aka jinkirta 170 da soke 27 daga tashin jiragensa.
Duk da haka, Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Venezuela ta nemi kamfanonin jiragen sama na duniya da su ci gaba da zirga-zirgarsu cikin awanni 48, tana mai gargadin asarar izinin tashi sama a kasar, a cewar Kungiyar Sufurin Jiragen Sama ta Duniya (IATA).
Your Comment